Spain ta ci Jamhuriyar Czech 1-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Spain ta fara gasar nahiyar Turai ta bana da kafar dama

Tawagar kwallon kafa ta Spaniya wadda ke rike da kofin nahiyar Turai ta doke ta Jamhuriyar Czech daya mai ban haushi a karawar da suka yi ranar Litinin.

Spain din wadda ke harin lashe kofi na hudu na gasar ta ci kwallonta ne ta hannun Gerard Pique, daga bugun da Andres Iniesta ya yi masa.

Tun a farko Spain ta kai hare-hare ta hannun Alvaro Morata da Jordi Alba da kuma David Silva, sai dai ba ta samu damar cin kwallo ba.

Haka kuma Spain din ta yi sa'ar fitar da kwallon da aka kusan cinta, inda Cesc Fabregas ya cire kwallon da Theodor Gebre Selassie ya bugo da ka.

Daf ya rage Jamhuriyar Czech ta farke kwallon da aka ci ta, bayan da Vladimir Darida ya kai hari, amma David de Gea ya hanata shiga raga.

Spain za ta buga wasanta na gaba da Turkiya a ranar Juma'a, kuma a ranar ce Jamhuriyar Czech za ta fafata da Croatia.