Babu ''yan madigo' a tawagar Nigeria

Hakkin mallakar hoto The NFF
Image caption Kungiyar marubuta labaran wasanni ce a Oyo ta yi hira da Akinwunmi

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF ta wanke mataimakinta na daya Seyi Akinwunmi kan zargin madigo a tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria.

Hukumar ta ce wata kafar yada labarai ce ta yi kuren wallafa hakikanin hirar da aka yi da jami'in a jihar Oyo a ranar Litinin.

Sai dai kuma NFF ta ce Akinwummi ya yi bayani a takaice kan madigo a harkar kwallon kafar mata a Nigeria da matsalar da take sa ba'a samun masu daukar nauyin wasannin mata.

NFF ta ce Akinwumi cewa ya yi a hirar: "Na fuskanci akwai matsalar da muke cin karo da ita, idan muka zo neman kudin da za a dauki dawainiyar kwallon mata, ana amannar da akwai halin madigo a tare da su.

Hakan ne ya sa da yawan wadanda muke hulda da su ke tserewa daga daukar nauyin wasanninsu, saboda amannar madigo tattare da mata.

Dalilin da ya sa kenan suka gwammace kin daukar dawainiyar wasannin mata, domin kar a samesu da hannu a ciki".