Za a dakatar da Rasha daga Euro 2016

Magoya bayan Rasha Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hargitsin ya tayar da hankalin jama'a sosai

An dakatar da Rasha daga gasar cin kofin kasashen Turai, amma hukuncin zai fara aiki ne idan aka sake samun magoya bayan kungiyar kwallon kafar kasar da laifin tayar da hargitsi.

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (Uefa), ta kuma ci tarar kasar Yuro 150,000.

Hakan dai ya faru ne saboda hargitsin da magoyan kasar suka tayar a lokacin wasan da suka kara da Ingila a birnin Marseille ranar Asabar.

Uefa ta ce za a aiwatar da hukuncin da zarar irin wannan lamari ya sake faruwa a sauran wasannin da Rasha za ta buga.

A gefe guda kuma, an fara mayar da wasu magoyan kasar ta Rasha zuwa gida daga Faransa bayan hargitsin da ya yi ta faruwa a gasar ta Euro 2016.

Rasha za ta iya daukaka kara idan ba ta gamsu da hukuncin da aka yanke a kanta ba.

Ana kuma tuhumar wasu magoya bayan Rashan kan nuna banbancin launin fata da kuma yin wasan wuta a lokacin da ake murza-leda.