Xia ya gama sayen Aston Villa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Aston Villa za ta buga gasar Championship ta bana

Babban dan kasuwar China, Dakta Tony Xia, ya kammala sayen Aston Villa kan kudi fan miliyan 76.

Xia mai shekara 39, ya ci jarrabawar cancantar zama mai rike da kungiyar gasar Premier da ta league.

Tony din zai maye gurbin dan Amurka, Randy Lerner, wanda ya sayi Aston Villa kan kudi fan miliyan 62 da dubu dari shida a shekarar 2006.

Villa ta fadi daga gasar Premier a karon farko a kakar bana, kuma tuni ta dauki koci Roberto di Matteo domin tun karar gasar Championship.