Arsenal za ta fara Premier bana da Liverpool

EPL
Image caption Manya-manyan kociyoyin duniya za su fafata a gasar ta bana

Arsenal za ta fafata da Liverpool a wasan farko na gasar Premier ta bana a filin wasa na Emirates a ranar 13 ga watan Agusta.

Mai rike da kambun gasar Leicester City za ta yi tattaki ne zuwa Hull City.

Ba za a dade ba za a fafata tsakanin Jose Mourinho da Pep Guardiola, inda Man United da Man City za su kece-raini a Old Trafford a ranar 10 ga Satumba.

Ga jerin wasannin makon farko:

Arsenal v Liverpool

Bournemouth v Manchester United

Burnley v Swansea City

Chelsea v West Ham United

Crystal Palace v West Bromwich Albion

Everton v Tottenham Hotspur

Hull City v Leicester City

Manchester City v Sunderland

Middlesbrough v Stoke City

Southampton v Watford