Ba Nigeria a kwallon kwandon Olympic

Image caption Nigeria ba za ta samu wakilci a wasan kwallon kwando ta mata ba a gasar Olympic

An fitar da tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria daga wasannin neman gurbin shiga gasar kwallon kwando ta Olympics.

Nigeria ta yi rashin nasara ne bayan da Korea ta Kudu ta ci Belarus 66 da 65, kuma suka kai wasan daf da na kusa da karshe.

Hakan ne ya sa dukkan kasashen da suka fafata a rukuni na uku a Faransa suka kammala da maki uku-uku.

Da ace Belarus ce ta ci karawar Korea ta Kudu da Nigeria ta samu kai wa gasar Olympics da za a yi a cikin watan Agusta a Brazil.