An hana Rasha gwada 'yan wasanta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun a cikin shekarar 2015 aka dakatar da Rasha daga shiga manyan wasannin tsalle-tsalle

Hukumar hana shan abubuwa masu kara kuzari ta duniya, WADA ta hana Rasha gwada 'yan wasanta.

WADA ta dakatar da hukumar gwajin 'yan wasa masu shan kwayoyi masu sa kuzari ta Rasha da yin aikin, ko kuma ta hada ta da jami'an tsaro.

A kwanaki biyu da suka wuce aka fitar da wani rahoto kan ko za a iya barin 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje na Rasha su shiga wasannin Olympic na bana.

A cikin watan Nuwamba ne aka dakatar da 'yan wasan Rasha, bayan da wani rahoton WADA ya tabbatar da cewar yawancin 'yan wasan sun sha kwayoyi masu kara kuzari.

Babban jami'in hukumar wasan tsalle-tsalle da guje-gujen Rasha ya yi rokon da a ba su lokaci domin yin gagarumin sauye-sauye.