Murray ya samu nasara a kan Bedene

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Murray zai sake karawa da dan Birtaniya Kyle Edmund

Andy Murray ya samu nasara a kan Aljaz Bedene a gasar kwallon tennis da suka fafata a Queen's Club.

Murray ya samu nasara ne da ci 6-3 da 6-4, ya kuma kai wasan daf da na kusa da karshe.

Kuma wannan ce karawa ta farko da aka yi tsakanin 'yan wasan Birtaniya a babbar gasa, rabon da a yi hakan tun shekara 10.

Murray din zai buga wasan gaba ne da Kyle Edmund, wanda ya kai zagayen gaba bayan da Paul-Henri Mathieu ya fice daga gasar, sakamakon raunin da ya yi.