CAF: Enyimba za ta kara da Al Zamalek

Hakkin mallakar hoto enyimba stadium lmcnpfl twitter
Image caption Enyimba ce ta rage mai wakiltar Nigeria a gasar zakarun Afirka

A ranar Asabar za a fara buga wasannin farko na cikin rukuni a gasar cin kofin zakarun Afirka ta Caf Champions League.

Rukunin farko ne zai fara yin wasa tsakanin Zesco United ta Zambia da Al Ahly ta Masar.

Wasa na biyu kuwa za a yi shi ne tsakanin Asec Mimosas ta Ivory Coast da Wydad Athletic Club ta Morocco.

A kuma ranar Asabar din rukuni na biyu zai kara tsakanin Entente Sportive ta Algeria da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu.

Sai a ranar Lahadi ne Enyimba International ta Nigeria za ta karbi bakuncin Al Zamalek ta Masar.