Ingila ta doke Wales da ci 2-1

Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption Wales tana da maki hudu, yayin da Ingila ke da maki biyu

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta doke ta Wales da ci 2-1 a gasar cin kofin nahiyar Turai da suka yi a ranar Alhamis.

Wales ce ta fara zura kwallo a ragar Ingila ta hannun Gareth Bale, saura minti uku a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Jarmie Vardy, wanda ya shiga wasan daga baya ya farkewa Ingila tamaula.

Daf da za a tashi daga karawar Daniel Sturridge ya ci wa Ingila kwallo na biyu.

Da wannan sakamakon Ingila tana mataki na daya da maki shida a rukuni na biyu, bayan kammala wasanni biyu-biyu.

Slovakia da Wales kowacce tana da maki uku-uku, yayin da Rasha ce ta karshe a rukunin.

A ranar Litinin za a buga wasannin karshe na cikin rukunin, inda Rasha za ta kara da Wales, da kuma gumurzu tsakanin Slovakia da Ingila.