Jamus da Poland sun buga canjaras

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Jamus da Poland kowacce tana da maki hudu-hudu daga wasanni biyu da suka yi

Tawagar kwallon kafa ta Jamus da ta Poland sun tashi wasa babu ci a gasar cin kofin nahiyar Turai da suka yi a ranar Alhamis.

Da wannan sakamakon Jamus da Poland sun hada maki hudu-hudu a wasanni biyu da suka fafata a rukuni na uku na gasar.

Irenald ta Arewa tana da maki uku, bayan da ta doke Ukraine da ci 2-0 a ranar ta Alhamis.

Sai a ranar Talata rukuni na ukun zai yi wasanninsa na karshe, inda Ireland ta Arewa za ta fafata da Jamus.

Ita kuwa Ukraine wadda ba ta da maki ko daya za ta kece raini da Poland a ranar ta Talata.