Coe ya ci zabe mai takaddama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Coe sabon shugaban hukumar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ya karyata zarginsa da ake yi

BBC ta fahimci cewar Lord Coe ya ci zaben shugabancin hukumar wasan tsalle-tsalle da guje-guje da taimakon mutumin da ke da hannu kan zargin badakalar shan abubuwa masu kara kuzarin wasa.

A wani sakon kar-ta-kwana da BBC ta gani na wayar sadarwa ya ce tsohon jami'in tuntuba na hukumar tsalle-tsalle da guje-guje Papa Massata Diack ne ya samo wa Coe kuri'un da ya lashe zabe.

A cikin watan Agusta aka yi zaben hukumar, kuma tuni jami'an tsaro na kasa da kasa suke neman Papa Massata Diack ruwa a jallo.

Haka kuma a cikin sakon an yi amanar cewar Coe ya yi wa majalissar Birtaniya rufa-rufa.

Sai dai kuma sabon shugaban zakaran tseren mita 1500 ya karyata aikata ba dai-dai ba.