An raba jan kati 31 a Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto thenff
Image caption An kammala wasannin mako na 22 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Alkalan gasar Firimiyar Nigeria sun kori 'yan wasa 31 a wasanni 197 da aka yi a gasar.

Haka kuma alkalan sun raba katin gargadi ga 'yan wasan da suka yi laifi har guda 728.

Kungiyar Abia Warriors da Akwa United su ne kan gaba a yawan 'yan wasan da aka korar musu a gasar, inda aka ba su jan kati hudu-hudu.

Heartland kuwa 'yan wasanta uku aka bai wa jan kati, yayin da Rivers United da Lobi Stars da Sunshine Stars da Enyimba da Wikki Tourist da Nasarawa United suka karbi jan kati biyu-biyu.

Kungiyoyin da suka fi karbar katin gargadi sun hada da Nasarawa United da Rivers United, kowacce ta karbi guda 45.

Lobi Stars da Shooting Stars suna mataki na biyu, inda aka bai wa 'yan wasansu katin gargadi sau 44 kowaccensu.