Nicolas Gaitan ya koma Atletico Madrid

Nicolas Gaitan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gaitan yana haskakawa a Benfica

Kulob din Atletico Madrid ya amince da yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiya Nicolas Gaitan daga Benfica kan kudi yuro miliyan 25.

Dan kwallon mai shekaru 28, wanda aka alakanta da Manchester United, zai koma Atletico da murza-leda bayan kammala gasar Copa America.

A yanzu dan wasan yana Amurka ne inda yake takawa kasar Argentina leda a gasar.

Ya shafe kakar wasanni shida a Benfica, inda ya buga wasanni 200 sannan ya zura kwallaye 32.

Dan kwallon ya koma Benfica ne daga kungiyar Boca Juniors a 2010.

Gaitan ya lashe gasar Lig ta Portugal sau uku a jere, sannan kuma ya halarci wasan karshe na gasar Europa har sau biyu.