Murray ya lashe gasar Queen's Club ta biyar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Andy Murray ya lashe gasar ta Queens club ta biyar

Andy Murray ya zama dan kwallon tennis na farko da ya fi yawan lashe gasar Queen's Club, inda ya dauka sau biyar.

Murray ya samu wannan damar, bayan da ya doke Milos Raonic a dukkan karawa ukun da suka yi gumurzu.

Hakan ne ya sa ya lashe gasar ta Aegon Championships karo biyar, ya fara daukar kofin 2009 da 2011 da 2013 da 2015 da kuma 2016.

Murray din ya dara John McEnroe da Boris Becker da Roy Emerson a matsayin wanda ya fi yawan lashe gasar.