Faransa da Switzerlan sun kai zagayen gaba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Faransa da Switzerland sun kai wasan zagaye na biyu a gasar nahiyar Turai

Mai masaukin baki Faransa da Switzerland sun kai wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai bayan da suka buga 0-0

Hakan ya sa Faransa ta jagoranci rukuni na farko da maki bakwai, yayin da Switzerland ta yi ta biyu da maki biyar.

Romania kuwa daya mai ban haushi ta ci Albaniya, dalilin da ya sa ta hada maki hudu kenan a gasar, Albania kuwa ba ta da maki.

A ranar Asabar ake sa ran fara wasannin zagaye na biyu na gasar cin kofin nahiyar ta Turai.