Wikki Tourists ta ci Kano Pillars 3-1

Hakkin mallakar hoto LMC Facebook
Image caption Wikki Tourists ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Firimiyar Nigeria

Wikki Tourists da doke Kano Pillars da ci 3-1 a gasar Firimiyar Nigeria, wasan mako na 23 da suka yi ranar Lahadi.

Kano Pillars ce ta fara cin Wikki saura minti 10 a je hutun rabin lokaci ta hannun Emmanuel Edmund.

Ibramin Hassan ne ya farkewa Wikki kwallon da aka zura mata a minti na 77 ana taka-leda.

Wikki Tourists ta ci kwallo na biyu a bugun fenariti saura minti biyar a tashi daga karawar ta hannun Abubakar Lawan.

Daf kuma da za a tashi daga daga wasan na hamayya Wikki ta ci ta uku a bugun tazara ta hannun Ibrahim Alhassan.

Pillars ta karasa gumurzun da 'yan wasa takwas a cikin fili bayan da aka korar mata Jamiu Alimi da Tijjani Adamu da Rabiu Shehu.

Ga sakamaon wasu wasannin mako na 23 da aka yi:
  • Ifeanyiubah 2-0 Rivers Utd
  • MFM 0-1 Shooting Stars
  • Akwa Utd 2-0 El-Kanemi
  • Tornadoes 1-1 Rangers
  • Abia Warriors 1-0 Heartland