Wales da Ingila sun kai zagayen gaba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wales da Ingila sun kai wasan zagaye na biyu a gasar zakarun Turai

Tawagar kwallon kafa ta Wales da ta Ingila sun kai wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai da ake yi a Faransa.

Wales ta samu wannan damar ce, bayan da ta doke Rasha da ci 3-0 a fafatawar da suka yi a ranar Litinin.

Hakan ne ya sa Wales ta jagoranci rukuni na biyu da maki shida daga wasanni uku da ta kara.

Ita kuwa Ingila ta kai zagaye na biyu a gasar duk da tashi wasa babu ci tsakaninta da Slovakia.

Ingila ta kammala wasanninta uku na cikin rukuni da maki biyar, wanda hakan ne ya sa ta kai bantenta.

Slovakia kuwa ta kammala ne a mataki na uku da maki uku, yayin da Rasha ce ta karshe da maki daya kacal.