Inter Milan za ta sayi Yaya Toure

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Toure ya yi aiki da Guardiola a kungiyar Barcelona

Inter Milan na shirin taya dan kwallon Manchester City, Yaya Toure, domin ya buga mata tamaula.

Toure dan kwallon Ivory Coast, mai shekara 33, yana da sauran yarjejeniyar shekara daya a Ettihad.

Pep Guardiola ne ya sayar da Toure daga Barcelona zuwa City a shekarar 2010, karkashin Roberto Mancini.

Har yanzu City ba ta gabatar da Guardiola ga magoya bayanta ba, a matsayin sabon kociyanta.

Tuni kuma kocin ya sayo Ilkay Gundogan kan kudi fan miliyan 20 daga Borussia Dortmund.