Dattijon da ya ci kwallo a tarihin tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shekara 31 Miura yana buga gasar kasar Japan

Kazuyoshi Miura ya karya tarihin da ya kafa na dattijon da ya ci kwallo a fagen tamaula lokacin da ya buga gasar kasar Japan.

Miura ya zura kwallon ne a ranar Lahadi, inda ya ci wa FC Yokohama a minti na 22, duk da rashin nasar da suka yi 2-1 a hannun FC Gifu.

Hakan ne ya sa ya kafa tarihin dattijon da ya ci kwallo a wasan tamaula yana da shekara 49 da haihuwa da watanni uku da kwanaki 24.

Dattijon yana buga gasar Japan, wanda ya tsawaita zamansa a FC Yokohama, kuma kakar wasa ta 31 kenan yana murza-leda.

Miura ya ci wa tawagar Japan kwallaye 55 a wasanni 89, tun lokacin da ya fara yi mata wasa a 1990, amma bai taba buga mata gasar cin kofin duniya ba.

Dattijon da ke rike da tarihin cin kwallo a gasar J-League shi ne Zico, wanda ya ci wa Kashima Antlers tamaula yana da shekara 41 a shekarar 1994.