Tottenham za ta sayi Victor Wanyama

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Tun a bara Southampton ta umarci Wanyama ya nemi wata kungiyar da zai koma taka-leda

Tottenham ta amince ta sayi dan kwallon Southampton, Victor Wanyama, kan kudi fam miliyan 11.

BBC ta fahimci cewar Wanyama, dan wasan tawagar Kenya zai je White Hart Lane domin a duba lafiyarsa.

Dan wasan mai shekara 24 ya koma Southampton da murza-leda kan kudi fan miliyan 12 da dubu 500 a shekarar 2013.

Wanyama wanda ya buga wa Southampton wasannin League sau 85 ya kuma ci kwallaye hudu, zai taka leda a karkashin koci Mauricio Pochettino wanda ya horar da shi a Southampton.