An ci tarar Hungary kan hargitsin 'yan kallo

Image caption 'Yan kallo sun jawo hargitsi sau da dama a lokacin wasan Euro 2016

Kungiyar kwallon kafar Turai Uefa ta ci tarar Hungary fam dubu 50 saboda hargitsin da magoya bayanta suka nuna a wajen wasan cin kwallon kafar Turai Euro 2016.

An ci tarar hukumar kwallon kafar Hungary saboda hargitsin 'yan kallo da harba tartsatsin wuta da jefa abubuwa filin wasa a lokacin da kasar ta yi canjaras da kasar Iceland.

Hungary ce kan gaba a rukunin F kuma za ta fafata da Portugal ranar Asabar a wasansu na karshe na wannan rukunin.

A baya ma an ci tarar Crotia fam dubu 77 da kuma Rasha fam dubu 115 bayan da 'yan kallo suka jawo hargitsi yayin wasannin da ake a Faransa.

Zuwa yanzu dai Uefa ta ci tarar kasashe takwas sakamakon hargitsin da magiya baya ke jawowa, da suka hada da Albania da Romaniya da Turkiyya da Belgium da kuma Portugal, kuma suna fuskantar ladabtarwa.