Ibrahimovic zai yi ritaya bayan Euro 2016

Hakkin mallakar hoto UEFA handout

Dan wasan gaban Sweden, Zlatan Ibrahimovic, ya sanar da cewa zai yi ritaya daga buga wa tawagar Sweden tamaula, bayan gasar Euro 2016.

Sweden za ta fafata da Belgium a rukuni na biyar a gasar Turai a ranar Laraba, wanda ka iya kasancewa wasan da zai bugawa kasar na karshe.

Ya ce, ''Ina matukar alfahari game da abinda na cimma, kuma a ko da yaushe zan rika rike tutar Sweden tare da ni.''

An alakanta cewar dan wasan zai koma murza-leda a Manchester United, wanda yarjejeniyarsa ta kare da Paris St- Germain a kakar wasan bana.

Ana tsammanin zai wakilci kasarsa a wasannin Olympics da za a yi a Rio na kasar Argentina a cikin watan Agusta.