Leicester City ta sayi Luis Hernandez

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kungiyar kwallon kafar Leicester City ta sayi dan wasan Spain Luis Hernandez a kwantaragin shekara hudu, wanda zai fara ranar daya ga watan Yuli.

Dan wasan, mai shekara 27, zai je kungiyar ne a matsayin aro idan kwantaraginsa da Sporting Gijon ya kare.

Hernandez ya buga wa Sporting Gijon kwallon sau 140 a gasar tun lokacin da ya koma can a shekarar 2012.

Hernandez ya samu horo ne a gurbin matasa na Real Madrid ko da yake bai buga wa kungiyar wasa ba.