Pillars ta doke Gombe a kwallon kwando

Image caption Pillars din ta ci wasanni biyu a gasar ta zakaru takwas da ake yi a jihar Legas

Kungiyar kwallon kwando ta Kano Pillars ta doke ta Gombe Bulls da ci 75 da 55 a gasar zakaru takwas da suka kara a ranar Talata a jihar Legas.

Pillars din ta yi nasara a karo na biyu kenan, bayan da ta ci Oluyole Warriors da ci 91 da 39 a ranar Litinin.

Kungiyar ta Kano za ta buga wasan gaba da Royal Hoopers a ranar Laraba, wadda ta ci Oluyole Warriors da yammacin Talata.

Gombe Bulls kuwa za ta kara ne da Oluyole Warriors wadda ta yi rashin nasara a wasanninta biyu da ta fafata.