Jamus da Poland sun kai zagayen gaba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamus ce ta jagoranci rukuni na uku sai Poland a matsayi na biyu

Kasashen Jamus da Poland sun kai wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai da ake yi a Faransa.

Jamus ta samu wannan damar ce bayan da ta doke Ireland ta Arewa da ci daya mai ban haushi a wasan karshe na rukuni na uku da suka yi a ranar Talata.

Hakan ne ya sa ta jagoranci rukunin da maki bakwai daga wasanni uku da ta fafata.

Ita ma Poland ta kai wasannin zagayen gaba ne a gasar, bayan da ta doke tawagar Ukraine da ci daya da babu ko daya.

Da wannan sakamakon Poland tana matsayi na biyu a rukuni na uku itama da maki bakwai, Ireland ta Arewa da maki uku ta kammala, yayin da Ukraine ba ta da maki ko daya.