Hungary da Iceland da Portugal sun kai wasan gaba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hungary ce ta jagoranci rukunin tare da Iceland

Tawagar kwallon kafa ta Hungary da ta Portugal sun tashi wasa 3-3 a gasar cin kofin nahiyar Turai da suka kara a ranar Laraba.

Hungary ta ci kwallayenta ne ta hannun Zoltan Gera da Balazs Dzsudzsak da kuma Balazs Dzsudzsak.

Wadanda suka ci wa Portugal kwallaye sun hada da Nani da kuma Cristiano Ronaldo da ya ci biyu a karawar.

Ronaldo ya kafa tarihin dan wasan da ya ci kwallo a gasa hudu da ya buga a wasannin cin kofin nahiyar Turai.

Iceland kuwa 2-1 ta doke Austria, hakan ya sa Hungary ta jagoranci rukunin da maki biyar, sai Iceland ta biyu da maki biyar.

Portugal kuwa ta uku ta yi da maki uku, yayin da Austria ce ta karshe da maki daya kacal.