An ci Italia an fitar da Sweden a gasar kofin Turai

Hakkin mallakar hoto ge
Image caption Italy za ta kara da Spain a wasan zagaye na biyu na gasar

Tawagar Jamhuriyar Ireland ta doke ta Italia da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin nahiyar Turai da suka kara ranar Laraba.

Jamhuriyar Ireland ta ci kwallonta ne ta hannun Robbie Brady saura minti shida a tashi daga karawar.

Ita ma Belgium daya mai ban haushi ta ci Sweden, kuma Radja Nainggolan ne ya ci mata kwallon.

Da wannan sakamakon Italia ce ta jagoranci rukuni na shida da maki 6, sai Jamhuriyar Ireland da Belgium maki hudu-hudu kowaccen su.

Hakan ya sa Italiya da Jamhuriyar Ireland da kuma Belgium suka kai wasan zagaye na biyu na gasar, yayin da Sweden ta yi waje daga gasar.

A ranar Asabar za a fara wasannin zagaye na biyu, inda Switzerland za ta fafata da Poland.

Wales kuwa za ta kara ne da Ireland ta Arewa, sannan da kece raini tsakanin Croatia da Portugal.