Rory McIlroy ba zai shiga Olympic

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cutar ta Zika dai tana sa wa ana haifar yara da dan-kai.

Daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon golf, Rory Mcllroy, ya janye daga shiga gasar Olympic da za a yi a birnin Rio saboda tsoron kamuwa da kwayar cutar Zika.

A wata sanarwa da ya fitar, McIlroy ya ce ko da ya ke yiwuwar kamuwa da kwayar cutar ba shi da yawa, amma "iyalina sun fi komai a wuri na".

Janyewar da ya yi daga shiga gasar wani babban koma-baya ne ga wasan na golf, wanda za a yi a wajen gasar a karon farko tun daga shekarar 1904.

Cutar ta Zika dai tana sa wa ana haifar yara da dan-kai.

A farkon wannan watan ma, dan wasan tseren keke na Amurka Tejay van Garderen ya ce ba zai shiga gasar ba saboda tsoron cutar ta Zika.