U23: Nigeria za ta kara da Mexico

Hakkin mallakar hoto TheNFF twitter
Image caption Siasia ne yake horar da tawagar matasa 'yan kasa da shekara 23

Tawagar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Nigeria za ta buga wasan sada zumunta da ta Mexico.

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria ce ta bayar da sanarwar, inda ta ce Nigeria za ta ziyarci Mexico ranar 2 ga watan Yuni.

Kuma kasashen biyu za su kece raini ne da karfe 8:30 na yammaci agogon Mexico.

Bayan wasan sada zumunta da Mexico, tawagar ta Nigeria za ta isa Amurka domin ci gaba da yin atisaye.

Matasan na Nigeria za kuma su yi wasa da Charleston Battery a Atlanta ta Amurka ranar Asabar 16 ga watan Yuni.

Haka kuma Nigeriar za ta fafata da Honduras a wasan na sada zumunta ranar 27 ga watan Yuni.

Nigeria za ta fafata da Sweden da Colombia da Japan a gasar Olympics da za a yi a Brazil a bana.