Griezmann ya tsawaita zamansa a Atletico

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Antoine Griezmann zai ci gaba da murza-leda a Atletico

Antoine Griezmann ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da buga wa Atletico tamaula har zuwa karshen kakar wasan 2021.

Ana yi ta rade-radin cewa Griezmann mai shekara 25, wanda ya ci kwallaye 32 a wasanni 54 da ya yi wa Atletico, zai koma Premier da murza-leda a baya.

Dan wasan, mai buga wa tawagar Faransa gasar kofin nahiyar Turai ta bana, ya ci kwallo a karawar da tawagar ta doke Albania da ci 2-0.

A makon jiya ma Atletico ta amince ta dauki dan wasan Benfica, Nicolas Gaitan.