Chile za ta kara da Argentina a wasan karshe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saukar ruwa sama kamar da bakin kwarya ya kawo tsaiko a karawar

Chile za ta fafata da Argentina a wasan karshe a gasar Copa America, bayan da ta ci Colombia 2-0.

Charles Aranguiz da Jose Pedro Fuenzalida suka ci wa Chile kwallayen da suka ba ta damar kaiwa wasan karshe a gasar.

Karawar tsakanin Chile da Colombia ta gamu da tsaiko tsawon awa biyu sakamakon saukar ruwa kamar da bakin kwarya.

Fafatawar da za a yi tsakanin Chile da Argentina maimaici ne da suka yi a bara, inda Chile ta lashe kofin a bugun fenariti.

A kuma wasan neman matsayi na uku za a kara ne tsakanin Colombia da Amurka a ranar ta Lahadi.