Vardy ya fasa komawa Arsenal

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Vardy ya zura kwallo a wasan da Ingila ta doke Wales da ci 2-1.

Dan wasan Leicester City Jamie Vardy ya amince ya sabunta kwantaraginsa a kulob din.

Leicester City ya ce dan wasan mai shekara 29, wanda ya jagorance su wajen lashe gasar Premier ta bana, zai tsawaita zaman sa a kulob din zuwa shekara hudu.

Wata sanarwa da kulob din ya fitar ta ce, "Dukkan mu muna sa ran wannan sanarwar za ta kawo karshen rade-radin da ake yi kan makomar Jamie."

An dai yi ta watsa labaran da ke cewa Vardy na shirin komawa Arsenal kafin a fara gasar cin kofin Turai, Euro 2016.

Kulob din Arsenal ya so sayen dan wasan kafin a fara gasar, sai dai hakan ya gagara.

Vardy ya zura kwallo a wasan da Ingila ta doke Wales da ci 2-1.