An kori dan kwallo saboda ya yi tusa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alkalin wasa ya ce da gangan dan kwallon ya yi tusa a cikin filin

Wani alkalin wasan kwallon kafa a Sweden ya kori dan wasa daga filin bayan da ya yi tusa ana tsaka da tamaula.

Dan wasan, Adam Lindin Ljungkvist , mai tsare baya, ya yi tusar ne a lokacin da ake karawa tsakanin Järna SK da Pershagen SK.

Adam mai shekara 25, ya ce ya ji cikinsa ne ya baci, saboda haka ya saki tusar nan take, daga nan ne alkalin wasa ya ba shi katin gargadi duga biyu a jere ya kuma daga ma sa jan kati.

Ya kuma ce ya tambayi alkalin wasa cewar bai cancanta ba ne ya yi tusa a cikin fili? Sai alkalin ya ce "bai kamata ba."

Alkalin wasan, Dany Kako, ya ce ya kori dan wasan ne saboda da gangan dan kwallon ya yi tusar, wanda hakan bai kamata ba.

Kristoffer Linde wanda ke buga wa daya kungiyar wasa ya ce yana nesa, amma sai da ya ji karar tusar, abin ya ba shi mamaki domin bai taba ganin irin haka a lokacin wasa ba tunda ya fara buga tamaula yana da shekara takwas.