Azarenka ba za ta yi gasar Wimbledon ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Victoria Azarenka na fama da jinya karo da dama

Victoria Azarenka, wacce ta taba lashe manyan gasar kwallon tennis, ba za ta buga gasar Wimbledon ta bana ba.

Mahukuntan gasar ne suka sanar da hakan, inda suka ce 'yar wasan ta yi rauni a gwiwarta.

Rabon da Azarenka ta buga babbar gasar kwallon tennis tun a watan jiya a wasan French Open, lokacin da ta hakura da karawar da take yi da Karin Knapp.

Azerenka wanda ta ci gasar Australian Open a shekarar 2012 da kuma 2013, sau da dama ta kan yi fama da rauni.

Za a fara yin gasar Wimbledon ta bana a ranar Litinin.