Southampton ba ta zawarcin Pellegrini

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Pep Guardiola ne ya maye gurbin Pellegrini a Man City

Southampton ta ce ba za ta dauko tsohon kocin Manchester City, Manuel Pellegrini, domin ya horar da ita ba.

Pellegrini yana sha'awar ya karbi aikin, sai dai kuma Southampton na neman wani kocin da zai maye gurbin Ronald Koeman.

Ana rade-radin cewar Claude Puel, wanda ya bar aikin horar da Nice ta Faransa a bana ne zai karbi aikin koci a Southampton.

Haka kuma ana alakanta cewar mai horar da tawagar kwallon kafar Amurka, Jurgen Klinsmann shi ma yana cikin takara.

Sauran wadanda suke son a ba su aikin sun hada da kocin Bournemouth Eddie Howe, da David Moyes da Frank de Boer.

Ronald Koeman wanda ya horar da Southampton tamaula shekara biyu, ya koma aiki a kulob din Everton.