Tottenham ta taya Janssen na AZ Alkmaar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai

Kungiyar AZ Alkmaar ta Netherlands ta ki sallama tayin da Tottenham ta yi wa dan kwallonta Vincent Janssen.

Janssen mai shekara 22, shi ne ya jagoranci yawan cin kwallaye a gasar kasar da aka kammala, wanda ya ci guda 27.

Kungiyar ta AZ Alkmaar na son a biya ta sama da Yuro miliyan 16 kan dan kwallon, yayin da De Telegraaf ta ruwaito cewar Tootenham ta taya shi kan kudi sama da fan miliyan 14 ne.

Janssen ya ci kwallaye uku a wasanni biyar da ya buga wa tawagar Netherlands ciki har da wadda ya ci Ingila a karawar da suka samu nasara da ci 2-1 a Wembley a cikin watan Maris.