Belgium za ta kara da Wales a gasar Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Belgium za ta fafata da Wales a ranar Juma'a

Belgium ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta doke Hungary da ci 4-0.

Eden Hazard ne ya fara ci wa Belgium kwallo, sai Toby Alderweireld ya kara ta biyu a fafatawar.

Saura minti 10 a tashi daga wasan Eden Hazard ya kara ta uku a raga kuma ta biyu da ya ci a karawar, sannan Yannick Carrasco ya zura ta hudu a raga.

Hakan na nufin Belgium za ta yi gumurzu da Wales a wasan daf da na kusa da karshe a ranar Juma'a.