An kori Alaba daga alkalancin tamaula

Hakkin mallakar hoto thenff
Image caption Abiodun Alaba dan jihar Ogun ne tsohon alkalin wasan tamaula

Kwamitin alkalan wasa na Hukumar kwallon kafa ta Nigeria ya sallami Abiodun Alaba, daga alkalancin wasan kwallon kafar kasar nan take.

Kwamitin ya yanke wannan hukuncin ne bayan da ya yi taro kan yadda Alaba yake jagorantar wasannin Firimiyar kasar karo da dama.

Bayan taron, kwamitin ya samu Abiodun Alaba da kasa tsawatarwa 'yan wasa a karawar da aka yi tsakanin MFM da Shooting Stars a fafatawar da suka yi ranar 10 ga watan Yuni a jihar Legas.

Alkalin wasan ya kasa daukar mataki kan 'yan wasan da suka dinga harzuka a lokacin wasan, duk da taimako da ya dinga samu daga mataimakansa.

An taba dakatar da Abiodun daga alkalancin wasannin gasar kasar a bara kan irin wannan laifin da ya aikata.