Firimiyar Nigeria za ta yi wasanni a Spaniya

Image caption An kammala wasannin mako na 24 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Nigeria ta shirya halartar wasan sada zumunta da za ta yi da Valencia da Malaga.

Hukumar za ta zabi fitattun 'yan wasan gasar domin karawa da kungiyoyin na Spaniya a ranar 10 zuwa 13 ga watan Agusta.

Wannan yana daga cikin yarjejeniyar da hukumar gudanar da wasannin Firimiya Nigeria ta kulla da ta La Ligar Spaniya a cikin watan Afirilu.

Shugaban hukumar gasar ta Firimiyar Nigeria, Shehu Dikko, ya ce za su je wasannin ne tare da wasu shugabannin kungiyoyin Nigeria da masu horar da tamaula da alkalan wasa.

Haka kuma za a nuna wasannin a talabijojin Nigeria da kuma na Spaniya idan kungiyoyin sun zo fafatawa.