Kano Pillars ta ci Abia Warriors 5-0

Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption An kammala wasannin mako na 24 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Kano Pillars ta doke Abia Warriors da ci 5-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 24 da suka kara a ranar Lahadi.

Pillars din ta ci kwallayenta ta hannun Rabiu Ali da Rasaq Adegbite da kuma Bala Zakka tun kafin a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutun ne, Pillars ta kara kwallaye biyu ta hannun Rabiu Ali da kuma Nafiu Kabuga.

Ga sakamakon wasannin mako na 24 da aka yi:
  • Shooting Stars 2-2 FC Ifeanyiubah
  • Sunshine Stars 2-0 MFM
  • Kano Pillars 5-0 Abia Warriors
  • Plateau Utd 2-0 Wikki
  • Nasarawa Utd 1-0 Tornadoes
  • Rangers 2-1 Wolves
  • El-Kanemi 1-0 Lobi
  • Heartland 2-0 Akwa Utd