Southampton ta dauki Redmond

Hakkin mallakar hoto Nathan Redmond Twitter
Image caption Nathan Redmond ya yi wasa shekara uku a Norwich City

Southampton ta dauki dan kwallon Norwich City, Nathan Redmond, kan kudi fam miliyan 10.

Redmond dan wasan tawagar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 21 ya kulla yarjejeniyar shekara biyar a Southampton din.

Norwich wadda ta fadi daga buga gasar Premier da aka kammala ta sayi dan kwallon daga Birmingham City, kan kudi fam miliyan 3.2 a watan Yunin 2013.

Redmond mai shekara 22 ya yi wa Norwich wasanni 122 ya kuma ci kwallaye 13 a shekara uku da ya murza mata leda.