Iceland ta fitar da Ingila daga gasar Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila ba ta taba daukar kofin nahiyar Turai ba

Tawagar kwallon kafa ta Iceland ta doke ta Ingila da ci 2-1 a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin nahiyar Turai.

Ingila ce ta fara cin kwallo a bugun fenariti ta hannun Wayne Rooney minti biyar da fara wasa.

Minti daya tsakani Iceland ta farke ta hannun Ragnar Sigurdsson sannan ta kara ta biyu ta hannun Kolbeinn Sigthorsson.

Da wannan sakamakon Iceland za ta buga wasan daf da na kusa da karshe da Faransa a ranar Lahadi.