Messi ya daina buga wa Argentina kwallo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Messi ya barar da fenareti

Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga murza leda a kasashen duniya bayan ya zubar da fenareti a wasan da Chile ta buge Argentina, kana ta lashe Copa America.

Wannan dai shi ne karo na hudu da tawagar kwallon kafar kasar ke shan kashi a wasan karshe a cikin shekara tara.

Dan wasan, mai shekara 29, ya ce "Wasan kasashen duniya bai dace da ni ba. Don haka ba zan sake buga irin wannan wasa ba. Na yi bakin kokari na, amma abin bakin ciki shi ne yadda muka kasa daukar kofi."

Messi dai ya lashe Kofin La Liga da na Zakarun Turai hudu a wasannin da ya yi wa Barcelona.

Amma nasara daya kawai ya taba yi a wasannin da ya buga wa kasarsa, wato kyautar zinare a gasar Olympic ta shekarar 2008.