Wimbledon: Djokovic ya kai zagaye na biyu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Djokovic mai rike da kofin Wimbledon ya kai wasan zagaye na biyu

Novak Djokovic ya kai wasan zagaye na biyu a gasar kwallon tennis ta Wimbledon da aka fara a ranar Litinin.

Djokovic mai rike da kofin bara, ya kai wasan gaba ne bayan da ya ci James Ward da ci 6-0 da 7-6 da kuma 6-4.

Dan wasan wanda ya ci babbar gasar Austaliya da ta Faransa a bana, na fatan kare kambunsa a Birtaniya.

Sai a ranar Talata Andy Murray zai fara buga wasa a gasar.