Dembele ya koma Celtic da murza-leda

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dembele ne dan kwallo na farko da Celtic ta saya a bana

Moussa Dembele ya koma kungiyar Celtic da taka-leda, bayan da ta amince da tafiyar Stefan Scepovic zuwa Getafe.

Dembele dan wasan tawagar Faransa ta matasa 'yan kasa da shekara 20, yarjejeniyarsa ce ta kare da Fulham a bana.

Celtic ta sayar da Scepotiv mai shekara 26, ga Getafe wadda ya yi wa wasa aro tsawon shekara uku.

Dembele mai shekara 19, ya ci wa Fulham kwallaye 17 daga wasannin 46 da ya yi mata.

Shi ne kuma dan kwallo na farko da sabon koci Brendan Rodgers ya saya a Celtic din.