PSG ta nada Emery a matsayin kocinta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Litinin Blanc ya yi murabus daga horar da PSG

Paris St-Germain ta nada tsohon wanda ya horar da Sevilla kwallo Unai Emery, a matsayin sabon kociyanta.

Emery ya maye gurbin Laurent Blanc wanda ya horar da kungiyar shekara uku ya kuma yi murabus a ranar Litinin.

Kociyan mai shekara 44, ya dauki kofuna uku na Europa League a shekara uku da ya yi a Sevilla.

Emery ya buga tamaula a karamar gasar kasar Spaniya, daga baya ya koma aikin horar da kwallon kafa.