Hulk zai koma wasa a Shanghai SIPG

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hulk ya koma Zenith da murza-leda daga Porto

Dan kwallon Zenit St Petersburg, Hulk, zai koma taka leda a Shanghai SIPG, kan kudi fan miliyan 41 da dubu dari biyar.

Ana sa ran Hulk mai shekara 29, zai ziyarci China a ranar Laraba domin a duba lafiyar sa.

Hulk zai zama dan kwallon da aka saya a gasar ta China mafi tsada a tarihi, bayan da aka sayi Alex Teixeira kan kudi fan miliyan 38 da dubu dari hudu.

A cikin watan Maris hukumar kwallon kafa ta China ta sanar da cewar za ta zama daya daga cikin fitattun kasashen da suke kan gaba a taka leda a duniya nan da shekarar 2050.