Ingila za ta nada Southgate kocin rikon-kwarya

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Iceland ce ta ci Ingila 2-1 a gasar cin kofin nahiyar Turai

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, za ta nada Gareth Southgate a matsayin kociyan rikon-kwarya na tawagar kwallon kafar kasar.

Hukumar tana son ta dauko wanda zai maye gurbin Roy Hodgson ne wanda ya yi ritaya daga aikin a ranar Litinin.

Hodgson ya yi murabus ne daga aikin, bayan da ya horar da tawagar kwallon kafa ta Ingila tamaula shekara hudu.

Babban jami'in hukumar, Martin Glenn, ya ce za su kai wata guda suna neman wanda ya dace ya ja ragamar Ingila.

Ana kuma rade-radin cewar kocin Arsenal, Arsene Wenger, yana daga cikin wadanda ake sa rai za a bai wa aikin.