Poland za ta kara da Portugal a gasar Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Alhamis Poland da Portugal za su kece raini a wasan daf da na kusa da karshe

Poland da Portugal za su kece raini a gasar cin kofin nahiyar Turai wasan daf da na kusa da karshe a ranar Alhamis.

Poland ta kai wannan matakin ne, bayan da ta doke Switzerland a bugun fenariti da ci 5-4, bayan da suka tashi 1-1 a wasan zagaye na biyu.

Ita kuwa Portugal ta kai wasan daf da na kusa da karshe ne, bayan da ta ci Croatia daya mai ban haushi.

Wannan ne karo na uku da kasashen biyu za su kara a babbar gasar kwallon kafa.

Poland ta samu nasara a kan Portugal da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986.

Ita kuwa Portugal 4-0 ta doke Portugal a gasar cin kofin duniya da aka yi a shekarar 2002.